Mu Zagaya Duniya - An rantsar da Joe Biden a matsayin sabon shugaban Amurka na 46 don maye gurbin Donald Trump - a podcast by RFI

from 2021-01-23T10:41:21

:: ::


An yi bikin rantsar da zababben shugaban Amurka Joe Biden a matsayin shugaban kasa na 46, tare da mataimakiyar sa Kamala Harris a Majalisar dokokin Amurka.

Bikin da ya gudana a Majalisar dokoki Amurka kamar yadda aka saba, shine irin sa na farko da shugaba mai barin gado yaki halarta a cikin shekaru 150, ganin yadda shugaba Donald Trump ya haure takalman sa ya tashi zuwa Florida, bayan yayi jawabi a cibiyar soji ta ‘Joint Base Andrews’ inda ya shaidawa magoya bayan sa cewa zai sake dawowa ta wata hanyar, bayan nasarorin da yace ya samu.

Garba Aliyu Zaria a cikin shirin Mu zagaya Duniya ya mayar da hankali kan rantsar da sabon Shugaban Amurka Joe Biden,Shugaba na 46.

Further episodes of Mu Zagaya Duniya

Further podcasts by RFI

Website of RFI